Za'a yi garon bawul a gwamnatin Masar
April 29, 2012Shugaban majalisar mulkin Soji a Masar ya faɗa wa kakakin majalisa Sa'ad al-Katatni cewar, zai gudanar da garon bawul a gwamnati gabannin zaɓen shugaban ƙasar da zai gudana a watan gobe. Wannan sanarwa ta Field Marshal Hussein Tantawi, ta zo ne bayan da majalisar Masar dake da rinjayen jam'iyar 'yan uwa musulmi, ta dakatar da zama na mako guda, bisa ga ƙorafin sojoji sun ƙi mika wa jam'iyyarsu ragamar gwamnati. Zaɓen 'yan majalisar dokoki daya gudana a watan Janairu dai, ya ba wa jam'iyyu biyu masu kishin islama gagarumin rinjayen kashi biyu daga cikin uku na kujeru 498 dake majalisar Masar. Tun bayan nan ne reshen siyasa na 'yan uwa musulmi, ya fara matsin lamba wa majalisar mulkin sojin ƙasar, data mika musu ragamar shugabancin gwamnati. Sai dai majalisar sojin data karɓi mulki tun bayan hamɓarar da gwamnatin Hosni Mubarak a ranar 11 ga watan febrairun bara, na ci gaba da goyon bayan gwamnatin priminista Kamal al-Ganzuri. Ganzuri dai ya kasance minista a karkashin mulkin Mubarak, mutumin da masu kishin Islaman suka zarga da zagon juyin juya halin daya gudana a ƙasar.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Abdullahi Tanko Bala