1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za'a binciki tsohuwar gwamnatin Rupiah Banda a Zambiya

October 14, 2011

Sabon shugaban Zambiya Michael Sata ya lashi takobin yaƙar Rashawa

https://p.dw.com/p/12s3K
Hoto: AP
A jawabinsa na farko ga majalisar kasar, Sabon shugaban Zambiya Michael Sata yayi alkawarin kakkaɓe Zambiya daga cin haci da rashawa. Ya ce gwamanatinsa ba zata lamunci almundahana da dukiyar jama'a ba, a lokaci guda kuma ba zata yi ƙasa a gwiwa ba wajen hukunta dukkan wanda aka samu da laifi a tsohuwar gwamnatin ƙasar ba . Tun bayan daya lashe zaɓen shugaban ƙasa a ranar 20 ga watan Satumba dai, Shugaban na Zambiya bai ɓata lokaci wajen sanar da manufarsa na binciken jami'iyyar tsohuwar gwamnatin Rupiah Banda, data mulki ƙasar na tsawon shekaru 20 ba. Tuni dai Shugaba Sata ya tsige shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa Godfrey Kayukwa, wanda ake zargi da kasancewa na hannu daman tsohon shugaba Banda. Ƙungiyar yaƙi da cin hanci ta kasa ta kasa ta Transparency International da jami'iyyun adawar Zambia dai sun sha yin kira ga Kayukwa da yayi murabus.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Usman Shehu Usman