1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a yi wa Chadi da Afirka ta Tsakiya tsakani

June 2, 2021

Kasashen Chadi da Afirka ta Tsakiya sun bukaci sa hannun kungiyar Tarayyar Afirka ta AU da Majalisar Dinkin Duniya wajen binciken yadda aka sace tare da hallaka sojoji 6 a iyakokin kasashen guda biyu.

https://p.dw.com/p/3uLz5
Flagge der Afrikanischen Union
Hoto: Klaus Steinkamp/McPHOTO/imago images

Chadi dai ta zargi dakarun sojin Afirka ta Tsakiya da kisan sojojinta, lamarin da ya sanya ministoci uku na kasar ta Afirka ta Takiya yin tattaki ya zuwan Chadin a jiya Talata domin bin ba'asin abin da ya faru.

Da ma dai akwai wata jikakka tun a shekara ta 2013, bayan da Chadin ta shiga cikin kasashen kungiyar AU a lokacin da Afirka ta tsakiya ta shiga yakin basasa. Batun na Chadin na cikin abubuwan da kungiyar habbaka tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afirka ta ECCAS za su tattauna a babban taronsu da za fara a gobe.