1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a yi taro babban taro kan COVID-19

Ahmed Salisu
November 5, 2020

Majalisar Dinkin Duniya za ta gudanar da wani babban taro halin da ake ciki game da annobar coronavirus, bayan da kasashen duniya ke cigaba da samun sabbin masu kamuwa da cutar a kulli yaumin.

https://p.dw.com/p/3kvb5
Symbolbild Corona PCR Test
Hoto: picture-alliance/S. Simon

A dazu ne babba zauren Majalisar Dinkin Duniya din ya amince da yin wannan taro wanda zai hada kan shugabannin kasashen duniya da nufin tattauna matakan da za a dauka wajen dakile yaduwar cutar.

Gabannin wannan zama da ake sa ran yinsa tsakanin 3 da 4 ga watan Disamba dai, kasashen duniya ciki har da Jamus da Faransa da Ingila sun tsaurara matakan yaki da cutar inda Ingila ta sanya dokar kulle a fadin kasar baki daya.