Chadi: Za gurfanar da masu bore a gaba kotu
November 25, 2022Talla
Mutanen wadanda ake tsare da su tun a lokacin zanga-zangar nuna kyama ga gwamnatin Mahamat Idriss da 'yan adawar suka yi wacce a ciki fiye da mutane 50 suka mutu ana zarginsu da tayar da fitina. Za a gudanar da shari'ar ne kamar yadda ofishin mai shigar da kara na N'Djamena ya sanar a cikin gidan kurkukun da ake tsare da mutanen a Koro Toro, a tsakiyar hamada mai nisan sama da kilomita 600 a arewa maso gabashin babban birnin kasar.