Za a shirya sabon zaɓe a ƙasar Kirgistan
April 22, 2010Talla
Gwamnatin riƙon kwarya a ƙasar Kirgistan ta sanar da cewa za ta gudanar da zaɓen yan majalisar dokoki a ranar goma ga watan Oktoba mai zuwa, mataimakin friministan ƙasar Oumourbek Tekbaiev ya sheda cewa suna sa ran za a' game zaɓen yan majalisar da na shugaban ƙasa,sannan a cikin watan Yuni mai zuwa a gudanar da ƙuria'a jin ra'ayoyin jama'a akan kawo koskorima ga kundin tsarin mulki na ƙasar.Gwamnatin dai ta riƙon ƙwarya ta ce itace ke da cikkaken iko da mulki sannan kuma ta yi watsi da kallamun da hamɓararen shugaban mista Bakiev ya baiyana daga ƙasar Belarusiya inda ya ke gudun hijira cewa haryanzu shine cikkaken shugaba na Kirgistan.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi