1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yiwuwar kafa sabuwar gwamnati a Sudan

Zainab Mohammed Abubakar
October 29, 2021

Sabon jagoran mulkin sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya sanar da shirin nada sabon shugaban gwamnati cikin mako mai kamawa.

https://p.dw.com/p/42Lw1
Sudan |  Abdel Fattah Abdelrahman al-Burhan
Hoto: Mahmoud Hjaj /AA/picture alliance

A wata hira da yayi da kamfanin dillancin labaru na Rasha Ria Novosti, jagoran kifar da mulkin ya ce nan ba da jimawa za a zabi gogaggen ma'aikacin gwamnati a matsayin sabon shugaban gwamnati, wanda zai nada majalisar zartarwar da za ta mulki kasar.

A ranar Litinin dinnan ce dai sojoji suka kifar da mulkin wannan kasa ta yankin gabashin Afirka, biyo bayan rikicin siyasar da ya mamaye Sudan din. Janar Al-Burhan ya sanar da rusa gwamnatin rikon kwaryar kasar tare da kafa dokar ta baci.

Juyin mulkin na zuwa ne bayan makonni na zanga zangar adawa da gwamnatin wucin gadi a karkashin jagorancin Abdalla Hamdok, da wasu rigingimu na siyasa a Sudan din mai yawan al'umma miliyan 44.