Za a je zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa a Masar
May 26, 2012Talla
jam'iyar ta na buƙatar samin haɗin kai na sauran yan takaradomin daƙile yunƙurin mayar da hannun a gogo baya, na ceto juyin juya halin da yayi sanadiyar faduwar tsohohuwar gwamnatin mulkin kama karya ta Hosni Moubarak:
jami'yar ta yan uwa musulmi na baiyana haka ne sakamakon fafatarwa da za a yi a zaɓen shugaban ƙasar zagaye na biyu a cikin watan Yuni mai zuwa, tsakanin Muhammed Mursi da kuma Ahmad Chafig wanda tshohon minista ne a tsohuwar gwamnatin wanda shi ne ya zo na biyu a zagayen na farko.Sayed Mustafa jigo ne a jamiyyar ta yan uwa musulmi: ''ya ce a yanzu duk masu ra'ayin juyin juya hali, ya kamata su yi kokowar ganin an zaɓi Mohammed Morsi.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou