Za a hukunta masu amfani da makami mai guba a Siriya
January 23, 2018Sabuwar yarjejeniyar ta tanadi tuhumar mutanen da ake zargi da hannu a hare-haren makamai masu guba da aka yi ta kai wa a kasar Siriya, da kuma kalubalantar matakin Rasha na hawa kujerar naki a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a duk lokacin da kasashen duniya suka bukaci daukar mataki kan wannan matsala, kamar dai yadda ministan harakokin wajen Faransa Jean Yves le Drian ya yi karin bayani yana mai cewa:
"Mutanen da suka aikata wannan laifi sun san da cewa za su fuskancin doka ko badan-badade kuma za a hakunta su duk da tarnakin da matakin yake fuskanta a halin yanzu a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya"
Cimma wannan yarjejeniya ke da wuya, kasar Faransa ta sanar da kame kudan ajiya na banki na wasu kamfanonin kasashen Siriya da Faransa da Labanan da Chaina wadanda ake zargi da samar da kudaden shiga ga shirin kera makamai masu guba na gwamnatin Bashar al-Assad.
Wasu alkalumman kididdiga na kasar Faransa sun bayyana cewa an kai hari da makami mai guba akalla sau 130 a kasar ta Siriya daga shekara ta 2012 zuwa ta 2017.