1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba za a dage babban zaben Najeriya ba

Ramatu Garba Baba
February 8, 2023

Shugaban Hukumar Zaben Najeriya Farfesa Mahmoud Yakub ya ce, za a gudanar da zabukan kasar kamar yadda aka tsara yi a ranar 25 ga wannan watan na Fabrairu.

https://p.dw.com/p/4NG1i
Za a gudanar da babban zaben Najeriya a ranar 25 na watan Fabrairu
Za a gudanar da babban zaben Najeriya a ranar 25 na watan FabrairuHoto: Reuters/A. Sotunde

Babbar Hukumar Zaben Najeriya INEC, ta kauda fargabar da jama'a da dama ke yi na dage zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun Najeriya da za a gudanar a ranar 25 ga wannan watan na Fabrairu, tana mai cewa, za a gudanar da zaben kamar yadda aka tsara tun daga farko duk da matsaloli na karancin sabbin kudi da na man fetur da al'ummar kasar ke fuskanta a yanzu.

Shugaban hukumar Mahmood Yakub da ya halarci taron majalisar zartarwar kasar, a jawabinsa bayan ganawar ya ce, an shata matakan shawo kan wadannan kalubalen da ake ganin na neman kawo cikas ga zaben na 2023, musanman shirin Kamfanin man kasar na NNPC a wadata gidajen mai da fetur kafin zaben a yayin da ya ce, ya samu tabbaci daga Babban Bankin Najeriya kan cewa, ba za a bari batun sauyin takardun kudin ya shafi sha'anin zaben ba. 

Yan takara kimanin goma sha takwas ne ke neman kujerar shugabancin kasar, sai dai biyu na manyan jam'iyyun APC mai mulki da PDP mai adawa, sun sha zargin juna da hannu a halin kuncin da miliyoyin 'yan Najeriya ke ciki da suke zargin wani zagon kasa aka shirya wa wanda ke neman maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari.