1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a fuskanci karancin abinci a Yemen

August 22, 2019

Bayan alkawuran da kasashe suka yi na samar da kudaden agaji a Yemen, rashin samar da su na iya janyo matsala cikin dan karamin lokaci, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/3OIcj
Yemen Sanaa - Menschenmengen bei Essensausgabe
Hoto: Reuters/K. Abdullah

Hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya, ta yi gargadi kan yiwuwar fuskantar karancin abinci ga miliyoyin mutanen da ke fama da yaki a Yemen, muddin aka gaza samar da kudade cikin 'yan makonnin da ke tafe.

Mutane miliyan 12 ne dai ake batu a kansu ciki har da kananan yara da ke fama da rashin koshi akalla miliyan biyu da dubu 500.

Shugabar hukumar, Lise Grande, ta ce a halin da ake ciki sun ma dakatar da yi wa yara alluran rigakafi tun cikin watan Mayu, tare da barazanar cewa wasu ayyukan agaji 22 ma na kan hadarin tsayawa.

Cikin watan Fabrairu ne kasashen duniya suka yi alkawarin samar da dala biliyan biyu da miliyan 600 domin taimaka wa sama da mutum miliyan ashirin da ke fama a Yemen din.