1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen yan majalisun dokoki a Togo

October 14, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8Y

Yau ne al´ummar ƙasar Togo ke kaɗa ƙuri´ar zaɓen yan majalisun dokoki.

Tun bayan shekaru 17 da su ka wuce, wannan shine karo na farko, da jam´iyun ƙasar baki ɗaya, su ka shiga a dama da su, a cikin harakokin zaɓe.

Hatta da jam´iyar UFC ta madugun yan adawa, Gilchrist Olympio, ta amince ta shiga wannan zaɓe.

A jimilce, mutane kimanin milion 3 ya cencenta su kaɗa ƙuri´a a cikin rufunan zaɓe kusan dubu 6 a faɗin ƙasar baki ɗaya.

Yan takara 2.100, wanda su ka fito daga jam´iyun siyasa 32 su ka shiga gwagwarmayar samun nasara zaman yan majalisa.

Majalisar dokokin ƙasar Togo ta ƙunshi kujeru 81.

Masu sa ido ,daga ciki da wajen ƙasar Togo, su fiye da 3.500 ke duba yadda zaɓen ke wakana.

Hukumar zaɓe mai kanta, ta nunar da cewa, ta kammala dukkan shirye-shirye, a game da haka, bata da shakkun komai, zaɓen zai wakana lami lahia.

A nata ɓangare gwamnatin hadin kan ƙasar Togo ta alkwarta ɗaukar matakan adalci ta yadda sakamakon zaɓen zai sami tabaraki daga ɓangarorin daban daban.