Zaɓen yan majalisun dokoki a Burkina Faso
May 6, 2007Yau ne jama´a ƙasar Burkina Faso, ke zaɓen yan majalisun dokoki.
Baki ɗaya, kussan mutane milion4 da rabi, ya cencenta su kaɗa ƙuri´a domin zaɓen yan majalisu 111 daga jerin yan takara kussan dubu 4, da su ka hitto daga jam´iyun siyasa 47 na ƙasar.
Saidai akwai alamun jama´a na nuna halayen ko in kulla da wannan zaɓe , ta la´akari da yadda,har jajibirin zaɓe, mutane ƙalilan su ka karɓi katocin zaɓe ,inji shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta Musa Michel.
A tsawan kwanaki 21, na yaƙin neman zaɓe jama´iyun adawa, da su ka kasa haɗa kai, domin fuskantar jama´iyar shugaba Blaise Campaore, sun bayyana matsalolin da gawmanti mai ci yanzu, ta tsunduma jama´ar ƙasa a cikinsu.
Fatara da talauci, rashin kyaukayawan matakan tsaro, da al´ammuran cin hanci da karɓar rashawa injin yan adawar, sun zama ruwan dare a Burkina Faso.
A na kyauttata zaton bada sakamakon wannan zaɓe, ranar juma´a mai zuwa.