1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen yan majalisun dokoki a ƙasar Masar

November 25, 2011

Zaɓen zai kawo sauye sauye wajan naɗa fraministan wanda a da sarkin ne na Maroko ke naɗa shi

https://p.dw.com/p/13HCt
Sarkin Mohammed VI. na MarokoHoto: Mustpha Houbiss

Al'umma na kada ƙuriaa a zaɓen yan majalisun dokoki a kasar maroko, a zaɓen wanda ya biyo biyan gyaran fuska na kudin tsarin mulki da sarki Mmuahammed ya yi tun watanni biyar da suka gabata,ana sa ran kimani masu kaɗa kuria'a kamar dubu 13 da rabi ne zasu harlarci runfunan zaɓen.

A yanzu dai da wannan sabon kudin tsarin mulki jam'iyar da ta samu nasara a zaɓen yan majalisun dokokin ,ita ce za ta samu wakilcin naɗa framinista maimakon sarkin ya nada shi.Ana kyautata zaton cewar jami'yar PJD ta Abdellah Benkirane wacce ta ƙwashe shekaru da dama ta na adawa ita ce za ta samu nasara a zaɓen ,da ya zo a daidai lokacin da duban matasa ke gudanar da zanga zanga saboda rashin aikin yi ''wani matashin kennan ya na mai cewar muna buƙatar neman sauyi a wannan zaɓe''.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar