Zaɓen Siriya ya ci karo da harin bama-bamai
May 7, 2012Fashewar bama-bamai da faɗace faɗace a sassa daban daban na ƙasar Siriya suka mamaye zaɓen 'yan majalisar dokokin ƙasar da magoya bayan gwamnati suka yi a ranar Litinin. Magoya bayan 'yan adawa sun ƙaurace wa zaɓen da suka kwatanta shi da cewa dodorido ne kawai. Masu boren ƙin jinin gwamnatin shugaban Siriyar Bashar Al-Assad a wasu wurare a Daraa da kuma yankunan Ƙurdawa sun yi kira da a gudanar da yajin aiki na gama gari. Masu sa ido a zaɓen sun ce ba a samu kwararar mutane zuwa rumfunan zaɓe ba. Sai dai ma'aikatar cikin gida a birnin Damaskus ta ce mutane da yawa suka fita kaɗa ƙuri'a. A wani labarin kuma masu fafatuka sun ce dakarun gwamnati sun kashe mutane da yawa a lardunan Hassaka, Deir as-Saur, Homs da kuma Damaskus. A Daraa da Hama da wasu wurare an samu fashewar bama-bamai da tashe tashen hankula.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu