1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen raba gardama kan kudin tsarin mulki a Siriya

February 26, 2012

A ƙoƙarin kawo ƙarshen tashin hankali da ake fama da shi a ƙasar shugaba Bashar Al-Assad ya ɓulo da sauye sauye na siyasa

https://p.dw.com/p/14AIj
The picture of the Syria's President Bashar al-Assad is seen on central bank building in Damascus February 24, 2012. REUTERS/Khaled al-Hariri (SYRIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Hoto: Reuters

Rahotanin daga kasar Siriya na cewar al'umma ta fara kaɗa ƙuria'a a ranar ta farko na zaben raba gardama da ake gudanarwa a kan kudin tsarin mulki wanda zai ba da damar ƙaddamar da sauye sauye na siyasa.

Shugaba Bashar Al Assad shi ne ya ya gabatar da wannan tayi ga al'ummar kasar da ke yin borai na ƙin jinin gwamnatin sa domin samin ƙarin jam'iyyun siyasa.Sama da mutane miliyion 14 zasu kaɗa ƙuria'a a zaɓen da yan' adawa suka ƙauracewa waɗanda ke matsa ƙaimi ga shugaba Bashar Al Assad da ya yi marabus.Ana gudanar da zaɓen ne a cikin wani hali na tashin hankali wanda kawo yanzu ƙungiyoyin kare hakin bil adama suka ce an kashe a ƙalla mutane dubu 7600 a borai na neman sauyi na gwamnatin da yan adawar suke yi.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman