1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen raba gardama a Sudan

January 18, 2011

Ganin yadda akai ta samun matsaloli a shirye-shiryen zaɓen da kuma tsoron tashin hankali mai yawa a lokacin sa, masana ƙalilan ne su kai zaton zaɓen gaba ɗaya zai gudana cikin kwanciyar hankali.

https://p.dw.com/p/zzGb
Masu zaɓe a kudancin SudanHoto: picture alliance/dpa

A rahoton da ta bayar, tawagar ta yan kalllon ta ƙasa da ƙasa ta baiyana ƙarfin zuciya da farin cikin yadda aka tafiyar da zaɓen. Tawagar yan akallo ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Amerika, Jimmy Carter ta kwatanta zaɓen na kudancin Sudan a matsayin wanda ya dace da bukatu da sharuddan ƙasa da ƙasa tga fuskar demokraɗiya. To amma shugabnan tawagar yan kallo ta ƙungiyar hadin kan Turai, Veronique de Kayser, ta shaidawa tashar DW cewar a ra'ayin ta, yanzu lokaci bai yi ba da tawagar ta Carter zata bayar da irin wannan hukunci.

Tace ni kaina ban yi amfani da kalmomi kamar haka ba, saboda har yanzu mna tsakiyar al'amura ne, kuma shi kansa zaben na raba gardama ba'a kare shi ba tukuna. Maimakon haka, mun yi amfani da kalmomin zabe mai nagarta da aka yi shi cikin kwanciyar hankali, inda ɗimbin mutane suka fita domin kaɗa ƙuri'un su, abin dake nufin mun gamsu gaba ɗaya da irin abubuwan da muka gani, kuma wannan matakin farko ne mai armashi a game da zaɓen.

Jimmy Carter Kofi Annan Sudan
Tsofon shugaban Amirka Jimmy Carter da Uwargidansa a Juba.Hoto: AP

Kamar yadda yan kalllon na ƙasa da ƙasa suka nunar, zaben dai an yi shi ne cikin natsuwa da kwanciyar hankali, tare da kai takardun rajista da katunan zaɓe a mafi yawan runfunan zaɓen kan lokaci. Yan kallon sun kuma yabawa mafi yawan jami'an zaɓe saboda kyakkyawan aikin da suka yi, sun kuma lura da cewar an sami matsalar matsin lamba jefi-jefi ga masu kada kuri'u.

A kudancin wannan yanki, wadanda suka fita domin kada kuri'un su, sun kai kashi casa'in cikin dari na wadanda akai wa rajista. Hakan kuwa ya wuce adadin kashi sittin cikin dari da ake bukata kafin tabbatar dfa ingancin shirin gaba dayan sa. To sai dai a arewa, inda yan asalin kudancin Sudan suma aka basu damar zabe, ba'a sami wadanda suka kada kuri'un su da yawa ba. Josef Sayer shugaban ƙungiyar agaji ta Meseroer ta nan Jamus shima yana daga cikin waɗanda suka lura da yadda zaɓen na kudancin Sudan ya gudana.

GTZ Süd Sudan Kooperation
GTZ na taimakawa a kudancin SudanHoto: GTZ

Yace a arewa waɗanda suka fita domin yin zaɓen ba su taka kara sun karya ba, idan aka kwatanta da kudu. Ma'aikatan mu a arewa suka ce mutane yan ƙalilan ne suka yi zaɓen, saboda tsoron da suka nuna cewar jami'an tsaro suna lura da take-taken su, basu kuma da tabbas ma ko za'a ƙidaya ƙuri'un nasu idan suka kaɗa. Abin ya zama da wahala.

A ɗaya hannun kuma, halin da aka shiga a yankin Abyei yana ci gaba da kawo damuwa ga yan kallon na ƙasa da ƙasa. Mazauna wannan yanki a tsakanin arewa fa kudancin Sudan, an shirya zasu yi nasu zaben na raba gardama, game da inda suka fi son zama. To amma daga baya aka dakatar da zaben, sakamakon muhawarori da rashin jituwa a yankin shi kansa. Kudanci da arewacin Sudan ko wanne yana bukatar yankin ya kasance karkashin sa, saboda a can ne mafi yawan man fetur da ƙasar take da shi yake. Masu lura da al'amuran yau da kullum suka ce kudancin Sudan ba zai sami nasarar tabbatar da mulkin kansa ba, muddin ba'a daidaita makomar yankin Abyei ba.

Kakakin ƙungiyar haɗin kan Turai, Veronique de Kayser tace a bisa ra'ayin ta da kuma ra'ayin mafi yawan mazauna kudancin Sudan, Abyei wuri ne mai matuƙar muhimanci, dake iya tayar da wasu sabbin matsaloli. Saboda haka daidaita makomar sa abu ne da ya kamata a bashi matuƙar fifiko. Wannan ma shine abin da ta tattauna kansa da shugaban yankin kudancin Sudan, Sava Kiir da manyan yan siyasa na wannan yanki.

Mawallafa: Daniel Pelz/Umaru Aliyu
Edita: Ahmad Tijani Lawal