1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zaman zulumi a kasar Libiya

December 21, 2021

Ana fargaba da zaman zullumi kan yuwuwar barkewar tashin hankali a Libiya gabanin tabbatar da soke gudanar da zaben shugaban kasa a hukumance da ake tsammani.

https://p.dw.com/p/44fKb
Libyen | Checkpoint von Soldaten in Tripolis
Hoto: Mahmud Turkia/AFP/Getty Images

Ana zaman zulumi a  birnin Tripoli na kasar Libya a yayin da ake kyautata zaton hukumar zaben kasar ta sanar da dage zaben shugaban kasar da aka shirya gudanarwa nan da kwanaki uku. Gidan Talabijin na Aljazeera ya ruwaito cewa ya samu kwafin takardar hukumar zaben Libiya da take shirin rusa kwamitin da aka dora wa alhakin gudanar da zaben mai cike da takaddama.

Kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP, ya ce lamarin ya haifar da zaman dar-dar da ya kai rufe jami'o'i da sauran muhimman wurare don kauce wa tashin hankalin da ake zullumin ka iya biyo baya. Rahotanni sun ce an ga alamun bangarorin da ke yaki da juna a kasar ta Libiya da ke yankin arewacin Afirka sun fara tura gungun mayakansu dauke da muggan makamai a wasu unguwanni a birnin Tripoli.