1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin murƙushe adawa a Siriya

May 8, 2011

Sojojin siriya sun harbe mutane shida har lahira a birnin Banias da ke yankin arewa maso yammacin ƙasar lokacin yunƙurin murƙushe zanga-zangar ƙin jinin gwamnatin Bachar al-Assad.

https://p.dw.com/p/11BVP
ƙorafin masu zanga-zangan Banias kan amfani da tankokin yaƙi a SyriyaHoto: AP

Masu fafutukar kare hakkin bil Adama na ƙasar Siriya sun bayyana cewa mutane shida sun rasa rayukansu a birnin Banias a lokacin da dakarun gwamnatin suka far ma waɗanda ke zanga- zangar ƙin jinin gwamnati. Huɗu daga cikin waɗanda aka harbe har lahira mata ne da ke neman a sako dubban mutane da aka kama da suna tayar da ƙayar baya. Tankokin yaƙi da aka kiyasta sun kai goma na ci gaba da sintiri a birnin na Banias da ke yankin arewa maso yammacin ƙasar ta Siriya.

ƙungiyoyi kare hakkin bil Adama sun ce akalla mutane 26 sun mutu a ranar juma'a yayin zanga- zangar da ta gudana a faɗin ƙasar da nufin nuna ƙyama ga salon mulkin shugaba Bachar al- Assad. ƙungiyar Tarayar Turai ta haramta sayar da makamai ga Siriya tare da ƙaƙaba wa wasu jami'an gwamnatin ƙasar guda 13 haramcin tafiye-tafiye da kuma taɓa kadarorinsu dake a waje . Amirka ana ɓangaren ta sake barazanar daukar sabbin matakan takura wa gwamnatin Siriya sakamakon amfani da ƙarfi fiye da kima da ta ke ci gaba da yi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi