1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yunwa ta halaka daruruwan mutane a arewacin kasar Habasha

January 31, 2024

Tsaninin karancin abinci ya yi sanadiyyar salwantar rayukan al'uma da ke zaune a arewacin Habasha. Sai dai a gefe guda gwamnati na musanta bayanan da ke nuna hakan.

https://p.dw.com/p/4btJy
Hoto: Million Haileselassie Brhane/DW

Akalla mutane 400 ne suka mutu sakamakon tsananin yunwa a yankunan Tigray da Amhara da ke arewacin Habasha.

Adadin da aka tattara cikin watannin da suka gabata, sun zo ne bayan wasu rahotannin sun nuna yadda mazauna yankunan na arewacin Habasha suka ba da labarin mutuwar gommai.

Sai dai kuma gwamnatin kasar Habasha ta musanata cewa wannan adadi na mutanen su ne suka rasa rayukansu.

Gwamnatin ta ce mutum 351 ne yunwa ta halaka a yankin Tigray cikin tsukin watanni shida.

A tsakiyar watan Maris na bara ne dai Majalisar Dinkin Duniya da Amurka suka dakatar da agajin abinci a yankin, bayan gano wani shiri na sace abincin da suke samarwa saboda jinkai.