1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Oxfam: Mutane miliyan 48 na fama da yunwa

Abdoulaye Mamane Amadou
September 16, 2022

Kungiyar agaji ta kasa da kasa Oxfam ta ce sauyin yanayi ne musabbabin karancin abinci da kasashen duniya ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/4GztE
Uk Oxfam-Sex-Skandal | Logo
Hoto: picture alliance/AP Photo/N. Ansell

Mutane miliyan 48 ne ke fama da matsalar yunwa sakamakon sauyin yanayi a wasu kasashen duniya, in ji wani rahoton da kungiyar agaji ta Oxfam ta fitar a wannan Juma'ar.

Rahoton yace barazanar karancin cimaka na dada karuwa a wasu kasashe shida da suka hada da Somaliya da Haïti da Djibouti da Kenya da Afghanistan da Guatemala da Madagascar da Zimbabwe da Nijar da kuma Burkina Faso, adadin da ya kara ninkawa idan aka kwatanta da miliyan 21 da aka samu a baya, a shekarar 2016.