1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Macron da Scholz sun tattauna da Putin

Abdoulaye Mamane Amadou
March 12, 2022

A yayin da aka shiga mako na uku na mamayar da Rasha take yi a Ukraine shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da Emamanuel Macron na Faransa sun tattauna ta wayar tarho da Vladimir Putin.

https://p.dw.com/p/48Och
Kombobild Vladimir Putin - Olaf Scholz - Emmanuel Macron

Shugabannin biyu sun sake nanata matsayinsu na ganin an kawo karshen mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine, tare da tsagaita luguden wuta a cikin gaggawa don kai dauki ga fararen hular da yakin ya rutsa da su.

Ko a wannan Alhamis da ta gabata shugabannin biyu sun tattauna da takwaransu na Vladimir putin kan batun dakatar da mamayar da Rashar ke yi wa Ukraine.

Fadar l'Elysée ta Faransa ta ce shugaba Macron ya tattauna har sau tara kenan ta wayar tarho da takwaransa na Rasha tun bayan barkewar rikicin da zummar lalubo hanyoyin warware shi cikin ruwan sanyi.