1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin kafa gwamnatin wucin gadi na farar hula a Masar

November 27, 2011

Mohammed El Baradei daya daga cikin masu zawarcin kujerar shugabancin Masar ya ce zai janye takararsa idan har aka ba shi damar jagorantar sabuwar majalisar rikon kwaryar kasar da ake neman a kafa

https://p.dw.com/p/13Hy3
Mohamed El BaradeiHoto: picture-alliance/dpa

Dan takarar shugaban kasa a Masar Mohammed El baradei ya yi tayin jagorantar gwamnatin hadin gambizar kasar abun da ya kara matsin kaimi ga gwamnatin sojin kasar a daidai lokacin da ake cigaba da zanga-zangar neman ganin karshen gwamnatin sojin a duk fadin kasar. Masu fafutuka na kira ga alummar kasar da ta sake fitowa kwan ta da kwarkwatarta zuwa dandalin Tahrir a wannan lahadin, wuni guda kafin gudanar da zaben da rikicin siyasa da yiwuwar barkewar rikici ke barazana ga gudanar da shi. Elbaradei na samun goyon masu fafutukar mayar da kasar bisa turbar demokradiyya to sai dai ga wasu, ba shi masaniya sosai dangane da siyasar kasar wacce ke tattare da sarkakiya kasancewar ya dade yana aiki a ketare a hukumar kula da makamashi ta Majalisar Dinkin Duniya. To sai dai a jiya asabar, ofishin yakin neman zabensa ya bada sanarwar cewa El baradei zai iya janye takararsa idan har kasar ta amince ya jagoranci sabuwar gwamnatin rikon kwaryar da za'a girka

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita: Mohammad Awal Nasiru