1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin duniya na inganta ilimi a Afirka

Salissou Boukari
February 3, 2018

Manyan kasashen duniya sun sha alwashin kara taimakon da suke bayarwa don bai wa yara kanana ilimi a kasashen Afirka. Mataki an dauke shi ne a babban taro kan harkokin ilimi a birnin Dakar na kasar Senegal.

https://p.dw.com/p/2s4JW
Senegal Schulklasse in Dakar
Wata makatantar boko a birnin Dakar na kasar SenegalHoto: DW/M. lamine Ba

Taron da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya halarta ya kuma samu halartar shahararriyar mawakiyar nan  da ake kira Rihana wadda ke a matsayin jakadiyar tsarin samar da ilimin na PME. Kasar Faransa ce tare da Senegal ke jagorancin babban zaman taron neman kudaden inganta tsarin nan na samar da ilimi na PME, inda a cewar kasar Faransa wannan tsari na bisa kan hanyarsa ta bunkasa ilimi ganin zai iya samun kudaden da suka kai dalla miliyan dubu uku da digo daya kamar yadda aka sanar.

Wannan babban zaman taron ya samu halartar shugabannin kasashen Afirka akalla 10, kuma babbar mawakiyar nan Rihana da ta sha alwashin samar da miliyan 250 na Euro, ta nuna gamsuwarta da ci-gaban da aka samu, inda kasashe irin su Faransa, Birtaniya na Norwai suka sanar da bada karin tallafi.