Yunkurin cafke Ahmed Shafiq na Masar
September 11, 2012A wannan Talata, Gwamnatin ƙasar Masar ta bada sammaci kama tsohon Fira Ministan ƙasar Ahmed Shafiq, wanda kae zargi da cin hanci da rashawa, ƙarƙarshin gwamnatin Hosni Mubarak, da juyin juya hali ya yi awun gaba da ita. Ana zargin tsohon PMn da hanu cikin cin hanci da 'ya'yan Mubarak Alaa da Gamal su ka yi, lokacin mulkin mahaifinsu.
Majiyoyin shariyar ƙasar sun tabbatar da labarin, kuma yanzu haka Shafiq yana zama a haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, tun lokacin da shugaba Mohamed Mursi ya kada shi a zaɓen da ya gabata.Ahmed Shafiq tsohon babban habsan sojan saman ƙasar ta Masar kuma tsohon ministan sufurin jiragen sama, ya zama Fira Minista a farkon boren da ya yi sanadiyar kawo ƙarshen mulkin Hosni Mubarak, a shekara ta 2011.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammadou Awal Balarabe