1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin MDD na ladabtar da su Sudan

May 1, 2012

Mamabobin Kwamitin sulhu na MDD sun kasa cimma matsaya game da matakan da ya kamata a ɗauka kan Sudan da sudan ta Kudu bayan da ƙasar China ta nuna adawa.

https://p.dw.com/p/14nYc
The United Nations Security Council meets at the United Nations in New York to discuss the ongoing violence in Syria April 21, 2012. The U.N. Security Council unanimously adopted a resolution on Saturday that authorizes an initial deployment of up to 300 unarmed military observers to Syria for three months to monitor a fragile week-old ceasefire in a 13-month old conflict. REUTERS/Allison Joyce (UNITED STATES - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Ƙasar china ta nuna adawa ga yunƙurin Amirka na neman ƙaƙaba wa Sudan da kuma Sudan ta kudu takunkumi sakamakon ƙin mutunta kirar da aka yi musu na kawo ƙarshen faɗa tsakaninsu. ita dai fadar mulki ta Beijing ta yi amfani da ƙarfin faɗa a jinta a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya wajen karya lagwon ƙudirin da ya tanadi tilasta wa maƙobtan biyu daina musayar wuta tsakanin Sudan da kuma Sudan ta kudu.

Amirka ta so kwamitin sulhu ya yi amfani da ƙarshen wa'adi da ƙungiyar Gamayyar Afirka ta ɗibar wa ƙasashen biyu domin ladabtar da su. Rasha ma dai ta yi ɗari-ɗari game da wannan ƙudiri da aka shafe sa'o'i ana tafka muhawara akan sa a birnin New-York. Jami'an dipolomasiya na sa ran Amirka za ta kwaskware ƙudirin nata game da Sudan kan nan da ranar laraba mai zuwa domin ta samu karɓuwa tsakanin mambobi 15 na kwamitin sulhu.

ƙungiyar Gamayyar Afirka(AU) ta tsayar da 25 ga watan Afirilu a matsayin ranar da ya kamata Sudan da kuma Sudan ta kudu su daina musayar harbe-harbe tsakaninsu, yayin da ta ɗibar musu watannin uku domin su cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninsu, ko kuma ta nuna fishinta.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Saleh Umar Saleh