1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin Amirka na canjin mulki a Siriya

August 11, 2012

Sakatariyar harkokin wajan Amirka Hillary Clinton ta ya da zango a ƙasar Turkiya domin tattaunawa da shugabannin kasar akan rikicin Siriya da kuma 'yan gudun hijira.

https://p.dw.com/p/15nx3
US Secretary of State Hillary Rodham Clinton speaks at news conference during the ministerial meeting of the Global Counterterrorism Forum in Istanbul, Turkey, Thursday, June 7, 2012. Clinton on Thursday condemned the Syrian government for new reports of "simply unconscionable" violence, accusing President Bashar Assad of intensifying a crackdown of a national uprising that has already killed thousands. (Foto:AP/dapd)
Hoto: AP

Hillary Clinton za ta ambato batun tallafa wa 'yan tawayen na Siriya tare da shugabanin Turkiya, da kuma maganar makomar ƙasar bayan faduwar gwamnatin Bachar al -Assad. Snnan da tabo zance agajin jin ƙai ga 'yan gudun hijiran na Siriya da ke makobciyar kasar.

Kusan 'yan gudun hijira 50.000 daga ƙasar ta Siriya suka kwarara zuwa Turkiyar tun lokacin da aka fara tashin hankalin na Siriya. A halin da ake ciki kuma faɗa na ƙara yin muni a unguwar Salhudine dake a birnin Aleppo inda 'yan tawaye suke yin yaƙin sari ka noƙe, bayan da suka janye tun canda farko.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe