1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yuganda ta kama wani jagoran 'yan ta'adda

May 19, 2024

Rundunar Sojin Yuganda, ta ce ta kama wani jagoran kungiyar 'yan ta'adda da ya kware wajen hada ababen fashewa da bama-baman da kungiyar ke kai munanan hare-hare a kasar.

https://p.dw.com/p/4g3Hz
Hoto: Alain Uaykani/Xinhua/picture alliance

An dai kama kasurgumin dan ta'addan, Anywari Al Iraq ne a wani daji da ke Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango inda nan ne maboyar kungiyar. A cikin sanarwar da rundunar ta fitar, ta ce sun ceto mutum tara ciki har da yara, a samamen da suka kai lardin Ituri da ke gabashin Kwango.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, an gano kayan hada ababen fashe wa da dama. Mayakan ADF da ke da mazauni a Kwango tun a shekarar 1990 na tawaye a Yuganda inda ake zarginsu da kashe daruruwan mazauna kauyuka a tsawon shekaru. A shekarar 2012 ce dakarun Yuganda suka yi hadin gwiwa da takwarorinsu na gabashin Kwango domin dakile ayyukan ta'addanci.