1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yoweri Museveni dan shekaru 74 zai sake tsayawa takara

Abdourahamane Hassane
April 18, 2019

Kotun koli a Yuganda ta amince da soke wani daftarin kudirin doka da ke kayade adadin shekaru 75 na tsayawa takara a zaben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/3H3Qa
Uganda Präsident Yoweri Museveni
Hoto: picture-alliance/dpa/I. Langsdon

Dokar wacce majalisar dokokin Yuganda ta amince da ita a karshen shekara ta 2017, za ta bai wa shugaba Yoweri Museveni  damar sake tsayawa takara a zaben shugaban kasa na shekara ta 2021. Shugaban na Yuganda yana a kan karagar mulki ne tun a shekara ta 1986.