1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yuganda: An tuhumi Bobi Wine da cin amanar kasa

Mohammad Nasiru Awal SB
August 23, 2018

Da farko a wannan Alhamis wata kotun soji a Yuganda ta dage tuhume-tuhume da ake wa Bobi Wine na mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

https://p.dw.com/p/33dg3
Bobi Wine wanda kuma ake kira shugaban unguwannin talakawa
Bobi Wine wanda kuma ake kira shugaban unguwannin talakawaHoto: Getty Images/AFP/I. Kasamani

A wannan Alhamis wata kotun majistire a kasar Yuganda ta tuhumi dan majalisar dokokin kasar na bangaren adawa da laifin cin amanar kasa dangane da rawar da ya taka a jifar da aka yi wa ayarin motocin shugaban kasa Yoweri Museveni a watan nan na Agusta.

Kotun ta bada umarni dan siyasar wanda shahararren mawaki ne, Robert Kyagulanyi Ssentamu, da ake wa lakabi da Bobi Wine, ya koma gidan wakafi har zuwa ranar 30 ga watan Agusta. Sai dai ta ba shi damar ganin likita saboda abin da ta kira rashin lafiyar wanda ake tuhumar.

A can kasar Kenya magoya bayanshi da suka hada da matasa 'yan siyasa na Kenya sun gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Yuganda da ke birnin Nairobi suna kira da a saki dan siyasar da sauran 'yan adawa da mahukuntan Yuganda ke tsare da su.

Boniface Mwangi dan siyasa ne kuma mai fafutuka na kasar Kenya.

"Bobi firsinan siyasa ne, kuma dan kwatar 'yanci ne. An kama shi saboda fadan gaskiyarsa. Saboda haka muke nuna masa zumunci, Bobi Wine na zama wakilin matasan Afirka da suka gaji da mulki irin na cin hanci da rashawa da kuma danniya."

Da farko a wannan Alhamis wata kotun soji ta dage tuhume-tuhume da ake wa Bobi Wine na mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.