1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Batun tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas

Suleiman Babayo MAB
February 8, 2024

Duk da matakin Isra'ila da adawa da shirin tsagaita wuta Sakataren harkokin wajen Amurka ya ce akwai yuwuwar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas.

https://p.dw.com/p/4c9aF
Sakataren harkokin kasashen katere na Amirka, Antony Blinken da Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila
Sakataren harkokin kasashen katere na Amirka, Antony Blinken da Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ilaHoto: Amos Ben-Gershom/dpa/picture alliance

Sakataren harkokin kasashen katere na Amurka Antony Blinken ya ce akwai damar samun yarjejeniya tsakanin Isra'ila da tsagerun kungiyar Hamas na Falasdinu domin tsagaita wuta inda haka zai janyo samun sakin 'yan Isra'ila da ake garkuwa da su. Shi dai Blinken ya bayyana haka lokacin ziyara a kasar ta Isra'ila.

Haka na zuwa bayan watsi da yuwuwar tsagaita wutar da Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya yi.

Tun da fari, kungiyar Hamas ta mai da martini ga bukatun da da Isra'ila da Amurka da masu shiga tsakani Qatar da Masar, suka gabatar, ta hanyar gabatar da nata daftarin tayin da ta nemi kasashen Masar da Qatar da Rasha da Turkiyya gami da Majalisar Dinkin Duniya, su zama shaidu da za su tabbatar da an aiwatar da yarjejeniyar sau da kafa.