1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawayen Yemen na fita daga Hodeida

Gazali Abdou Tasawa
December 29, 2018

Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da soma ficewar 'yan tawayen Houthi na Yemen daga birnin Hodeida kamar yadda yarjejeniyar da suka cimma da gwamnati ta tanada.

https://p.dw.com/p/3Aliz
Jemen Hafen von Hudaida
Hoto: Getty Images/AFP/Str

Kamfanin dillancin labaran Saba mai kusanci da 'yan tawayen na Houthi a kasar ta Yemen, ya ruwaito wani daga cikin jagororin 'yan tawayen na cewa tun da karfe 12 na daren Juma'a 28 ga wannan wata na Disamba ne, suka fara janyewar daga tashar jiragen ruwan birnin na Hodeida da ke zama babbar tashar da ake shigo da hajoji da kuma kayan agaji zuwa cikin kasar.

Yarjejeniyar da suka cimma a farkon watan nan na Disamba, ta kuma tanadi ficewar sojojin gwamnati daga yankunan birnin da suka sake karbewa daga 'yan tawayen, shekaru hudu bayan da mayakan na Houthi suka fatattake su daga cikinsa. Majalisar Dinkin Duniya dai ta aika da masu sa ido zuwa tashar ruwan ta Hodeida.