1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiya ta amince da kawo karshen rikicin Yemen

Lateefa Mustapha Ja'afarNovember 11, 2015

Ministan harkokin kasashen ketare na kasar Saudiya Adel al-Jubeir ya bayyana goyon bayansa da taron tattaunawa domin kawo karshen rikicin kasar Yemen.

https://p.dw.com/p/1H4FX
Hoto: picture-alliance/dpa/Y. Arhab

Jubeir ya bayyana goyon bayan nasa ne ga manema labarai jim kadan bayan kammala taron kasashen Larabawa da Amirka a birnin Riyadh na kasar Saudiyan. Ya kara da cewa suna goyon bayan taron kuma yana fatan za a shawo kan matsalar domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro da kuma daidaito a Yemne din. Majalisar Dinkin Duniya dai ta shirya gudanar da wani atro cikin wannan watan a birnin Geneva domin tattauna yadda za a kawo karshen rikicin da ya lakume rayuka da dama. Tun dai cikin watan Maris din da ya gabata ne Saudiya ta kaddamar da jagorantar kawayenta kasashen Larabawa wajen yin barin bama-bamai da jiragen yaki a Yemen din a kokarin da suka ce suna yi na fatattakar 'yan tawayen Huthi da ke kokarin raba gwaninsu Shugaba Abedrabbo Mansour Hadi da mulkin Yemen din.