1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yemen na fiskantar barazanar yunwa mai muni

Yusuf Bala Nayaya
October 24, 2018

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa a bayyane take kasar Yemen na fiskantar yanayi na yunwa mai munin gaske.

https://p.dw.com/p/374ke
Jemen |  Unterernährtes Kind
Hoto: picture-alliance/dpa/AA/M. Hamoud

Babban jami'i a Majalisar Dinkun Duniya Mark Lowcock ya fada wa Kwamitin Sulhu na MDD cewa yanayin da mutane da suka tsinci kai a kasar ta Yemen na yunwaya zamo mai munin da su kansu jami'an a aikinsu da suke fita kasashe ba su ga kamarsa ba.

Ya ce yanayin yawuce gargadin da suka yi kan barazanar ta yunwa a watan Nuwamba na shekarar 2017. Ya ce MDD a watan da ya gabata ta ce mutane miliyan 11 ne ke cikin tsananin bukatar abinci amma ya zuwa yanzu sun gano adadin ya kai mutane miliyan 14 adadin da ke zama kusan rabin al'ummar Yemen.