1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yemen: Fararen hula sun rasa ransu

Zulaiha Abubakar
November 6, 2018

Rahotanni daga kasar Yemen sun baiyana yadda wata arangama tsakanin 'yan tawaye da sojojin gwamnatin kasar a tashar jiragen ruwa dake birnin Hodeida ta yi sanadiyyar rasa rayukan fararen hula da dama.

https://p.dw.com/p/37lvc
Yemen - al-Hudaida - Soldat
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Gambrell

Cikin wannan makon ne dai asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cigaba da kai hare-hare a Hodeida zai kara jefa rayuwar al'ummar birnin a tsaka mai wuya. Ita dai tashar jiragen ruwa ta Hodeida na zaman cibiyar da kungiyoyin agaji suke sauke kayan abinci da magunguna don shigarwa cikin kasar ta Yemen inda cikin kowanne minti goma yaro daya ya ke mutuwa sakamakon tsananin yunwa.