1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yazidawa na fuskantar karancin abinci

August 17, 2014

Dubban Yazidawan Iraki da mamayar masu kaifin kishin addini ta sa suka kauracewa matsugunansu na fuskantar ja'ibar yunwa da karancin ruwan sha.

https://p.dw.com/p/1Cw1f
Irak Jesiden auf der Flucht Grenzbrücke
Hoto: Reuters

Rahotanni daga Iraki na cewar daruruwan Yazidawa ciki kuwa har da kananan yara wanda suka gujewa farmakin 'yan IS na cikin hadarin fuskantar yunwa saboda rashin isar kayan agaji musamman abinci da ruwan sha a inda suke gudun hijira.

Wata mata da ta zanta da kamfanin dillancin labarai na AFP ta ce sun yi da nasanin zuwa wajen saboda irin ukubar da suke fuskanta, inda ta kara da cewar gara ma da sun zauna a gida an kashe su da wannan hali da suke ciki.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da 'yan fafufutur ta IS da ke kokarin kafa daular Islama a Irakin suka hallaka kusan mutane 100 wadandan dukanninsu Yazidawan ne.

Mawallafi: Ahmed Salisu

Edita: Umaru Aliyu