1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawan haraji ya hana Bruno Labbadia horas da Super Eagles

Suleiman Babayo MAB
September 2, 2024

Rashin samun kason haraji da za ta biya gwamnatin Jamus, ya sa hukumar kwallon kafa ta Najeriya watsi da batun daukar Bruno Labbadia a matsayin babban kocin Super Eagles. Sannan muna dauke da wasannin lig na Bundesliga,

https://p.dw.com/p/4kBFX
Bruno LABBADIA ya jima yana horas da kungiyoyin kwallon kafa.
Bruno LABBADIA ya jima yana horas da kungiyoyin kwallon kafa.Hoto: Frank Hoermann/SvenSimon/picture alliance

Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Najeriya ta bayyana rashim cimma matsaya da Bruno Labbadia domin zama mai horas da 'yan wasan kwallon kafa na kasar. A farkon makon da ya gabata ne aka bayyana sunan Bajamushe Labbadia a matsayin sabon mai horas da 'yan wasan Najeriya. Daga bisa ne kuma shugaban hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Najeriya Ibrahim Gusau ya fitar da wata sanarwa inda yake cewa dokokin haraji na Jamus sun yi tarnaki wajen iya daukan Bruno Labbadia a matsayin mai horas da 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya, saboda ana bukatar hukumar NFF ta biya kimanin kashi 32 zuwa 40 cikin 100 na albashin mai haraswar a matsayin haraji ga gwamnatin Jamus.

Karin bayani: Sabon mai horas da 'yan wasan Super Eagles

Sakamakon wasannin da aka gudana a La Liga da Bundesliga

 VfB Stuttgart da FSV Mainz 05 sun tashin wasa ci 3-3
VfB Stuttgart da FSV Mainz 05 sun tashin wasa ci 3-3Hoto: Jan-Philipp Strobel/dpa/picture alliance

A La Liga da aka kara a kasar Sifaniya, Barcelona ta yi wa Valladolid cin kacar tsohon keke rakacau da ci 7 da 0, kuma Robert Lewandowski, Dani Olmo, Jules Koundé ne suka jefa kwallaye a raga. Sai dai Raphinha dan wasan gaba na Brazil ya zama zakara ga kungiyar ta Barcelona wajen jefa kwallaye uku daga cikin bakwai a ragar kungiyar ta Valladolid, yayin da Atletiko Madrid ta bi Athletic Bilbao har gida ta doke 1 da nema.

A wasanin lig na Jamus na Bundesliga da aka kara a karshen mako kuwa, ga sakamkon da aka samu:

Union Berlin 1 vs St. Pauli 0,  Stuttgart 3 vs Mainz 3,  Eintracht 3 vs Hoffenheim 1,  Bochum 0 vs Monchengladbach 2

Holstein Kiel 0 vs Wolfsburg 2,  Leverkusen 2 vs RB Leipzig 3,  Heidenheim 4, Augsburg 0,  Bremen 0 vs Dortmund 0

Gasar paralympics 2024 na ci gaba da gudana a Faransa

'Yar harbin kibiya Sheetal Devi ta kasar Faransa a gasar paralympics
Hoto: Jens Büttner/dpa/picture alliance

A wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya na masu bukata ta musamman da ke gudana a birnin Paris na kasar Faransa kuwa, ya zuwa yanzu kasar Chaina take matsayi na farko wajen lashe lambobi, yayin da Birtaniya take a matsayi na biyu, kana a matsayi na uku akwai kasar Brazil .sannan Amurka tana mataki na hudu. Inda ita kuwa kasar Ostareliya take a matsayi na biyar, a matsayi na shida a kai kasar Netherlands. Ita kuwa kasar Faransa mai masaukin baki ba yabo ba fallasa tana mataki na bakwai. Jamus a wannan karo tana a matsayi na 40.

An shiga mako na biyu da fara gasar kasa da kasa ta cin babban kofin shekarar 2024 na wasan kwallon Tennis da ake wa lakabi da U.S. Open a birnin New- York na kasar Amurika, inda 'yan wasa maza da mata suke nuna bajinta. wannan gasa dai, an shafe shekaru 56 ana yi a kasar ta Amurka: