Yawaitar kaurace wa zabe a tarayyar Najeriya
March 27, 2013A wani abun dake zaman gagarumin koma baya ga fagen siyasar tarrayar Najeriya, hukumar zaben kasar ta INEC ta ce ana samun gagarumin koma baya ga yawan al'umar Najeriya dake fita domin kada kuri'a a zabukan da hukumar ke yi yanzu haka.
A takarda dai tarrayar ta Najeriya ce ke zaman ta gaba ga batun masu zabe a daukacin nahiyar Afirka baki daya. Sama da 'yan kasar miliyan 60 ne dai hukumar zaben ta ce ta kai ga yi wa rijistar shiga cikin zaben kasar na shekara ta 2011.
To sai dai kuma sannu a hankali al'amura na sauyawa ga kasar da ta zura ido ta kalli dawowa daga rakiyar sabuwar demokradiyyar da mutanen kasar suka yi murnar tabbatarwa shekaru 14 da suka gabata.
Wani binciken hukumar zaben kasar ta INEC dai ya nuna matukar raguwar yawan masu fita domin kada kuri'unsu yayin zabuka a matakai daban daban na tarrayar Najeriya. Ga kasar da a baya ta rika samun kusan kaso 65-70 cikin 100 na masu kada kuri'ar tata na fitowa domin tabbatar da 'yancin su na zabar shugabanni.
Yawan masu fita kada kuri'a ya ragu matuka
Kasa da kaso 15 ne dai a cewar hukumar suka fito domin kada kuri'ar a yayin zaben kananan hukumomin da aka kammala a Abuja babban birnin kasar, a yayin da aka samu kaso 13 a jihar Yobe da ita ma ta kai ga zaben maye gurbi a cikin makon jiya.
Rahoton dai ya ambato dalilai kama daga na tsaron dake zaman na kan gaba ya zuwa na tunanin magudi yayin zabukan sannan kuma da rashin cika alkawuran 'yan siyasar kasar a matsayin muhimman dalilan al'ummar kasar na kaurace wa tsarin dake zaman matakin farko na demokradiyyar kasar da kuma a cewar Farfesa Lai Olurode dake zaman kwamishinan hukumar zaben kasar ta Najeriya ke zaman babbar matsala ga hukumar da ma demokradiyyar kasar.
"Ka dubi zaben Abuja na kwanan kasa da kaso 15 ne suka fito mun samu wani zaben cike gurbi a Yobe a makon jiya kasa da kaso 13 ne suka fito ba za ka ce INEC ba ce. In kuka janye kuka kyale 'yan kalilan suka yi zabe to kun kyale gwamnatin 'yan kalilan kuma wannan babban kalubale ne."
Kalubalen da zaben 2015 ka iya fuskanta
Sabon kalubalen dai na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke kara kusantar zabe cikin yanayi na tsoro da rashin tabbas sakamakon karuwar tashe tashen hankula da karuwar halin bera da kura daga ni sai 'ya'yana a tsakanin 'yan siyasar kasar. Ga tarrayar Najeriyar da ta kalli gagarumin koma bayar da ake ta'allakawa da mulkin soja.
To sai dai kuma a tunanin Lawalli Shu'aibu dake zaman sakataren jam'iyyar adawar kasar ta CAN wai in bera da sata to hukumar zaben kasar ta Najeriya ma da hannunta wajen warin da fagen siyasar kasar ke yi a yanzu.
"Ana dai kallon sabon salon kauracewar a matsayin abun dake iya shafar makomar shi kansa zaben shekara ta 2015 zaben da tuni aka fara nuna alamun raba gari a tsakanin sassan kasar daban daban."
To sai dai kuma a cewar Mallam Faruk BB Faruk dake zaman masanin harkokin siyasar Najeriya, guguwar siyasar za ta kai ga sauya tunanin al'umar kasar a cikin kankanen lokaci.
Abun jira a gani dai na zaman tasirin sabuwar matsalar dake iya kaiwa ga kara ruda fagen siyasar kasar dake rarrafen tashi a yanzu haka.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal