1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar tsaro tsakanin Amirka da Papua New Guinea

Suleiman Babayo ATB
May 22, 2023

Amirka ta karfafa tsaro da tsibirin Papua New Guinea inda bangarorin biyu suka amince da sabuwar yarjejeniyar tsaro abin da zai karfafa matsayin Amirka a yankin.

https://p.dw.com/p/4Rfby
Papua-New Guinea | Antony Blinken
Antony Blinken sakataren harkokin wajen AmirkaHoto: Andrew Kutan/AFP

Sakataren harkokin wajen Amirka, Antony Blinken ya isa kasar Papua New Guinea inda ya saka hannu kan sabuwar yarjejeniyar tsaro da tsibirin da ke arewacin kasar Australiya. Ita dai Amirka tana son nuna tasirin a yankin musamman yayin da take ci gaba da gasa da kasar Chaina wadda take neman samun karfin a yankin tekun Pacifik.

Yarjejeniyar za ta taimaka wajen karfafa matakan tsaro a yankin kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta tabbatar.

Shi kansa Firaminista James Marape na tsibirin na Papua New Guinea ya tabbatar da cewa suna kawance soja da Amirka tun fiye da shekaru 30 da suka gabata, daga shekarar 1989.