Yarjejeniyar tsaro tsakanin Masar da Isra'ila
August 26, 2011Talla
Masar da Isra'ila sun amince su ƙara adadin dakarun Masar da ke kan iyakar yankin Sinai bayan ɓarkewar wani rikici a yankin. Wani babban jami'in tsaro a yankin ya faɗawa kamfaninm dillancin labarun Reuters cewa bayan sun ɗauki lokaci suna tattaunawa yanzu ɓangarorin biyu sun amince da wata yarjejeniyar ƙara dakarun a tsakaninsu. An cimma wannan yarjejeniyar ce sakamakon matsalar tsaron da ake samu a kan iyakar, ko da yake jami'in wanda bai so a bayyana sunan sa ba ya ce sun harzanta yanke shawara dangane da matsalar ne bayan da wasu masu tada ƙayar baya suka harbe wasu mutane 'yan Israila guda 8, kuma Israila na zargin cewa maharan sun shigo ne ta zirin Gaza.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Mohammad Nasiru Awal