1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar tsagaita hari kan fararen hula

Abdullahi Tanko Bala
October 31, 2020

Kasashen Armenia da Azerbaijan sun amince ba za su kai hari da gangan akan fararen hula ba yayin da suke cigaba da gwabza fada a tsakaninsu akan yankin Nagorno-Karabakh.

https://p.dw.com/p/3kgWd
Berg-Karabach Konflikt
Hoto: Iliya Pitalev/Sputnik/dpa/picture alliance

Bangarorin biyu sun cimma wannan matsayar ce a tattaunawar sulhu da suka gudanar ranar Juma'a a birnin Geneva.

Kasashen biyu sun kuma amince za su yi musayar fursunonin yaki da kuma gawarwakin mutanen da aka kashe a filin daga nan da mako guda a cewar kungiyar kawancen tsaro da raya tattalin arzikin nahiyar Turai OSCE wadda ta jagoranci tattaunawar.

Hakan nan kuma bangarorin biyu za su mika tambayoyi da kuma bayanai a rubuce game da hanyoyin da suke gani sun fi dacewa don cimma tsagaita wuta bisa ka'idojin da aka amince da su a taron da ya gudana a Moscow a ranar 10 ga watan Oktoba.