1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Dakile kudaden fito tsakanin kasashen Turai da Japan

Suleiman Babayo USU
July 17, 2018

Kasashen Turai da Japan sun saka kulla yarjejeniyar dakile kudaden fito tsakanin bangarorin saboda bunkasa kasuwanci da mayar da martani kan sabbin manufofin Amirka.

https://p.dw.com/p/31b8c
Brüssel EU - Japan Gipfel
Hoto: picture-alliance/abaca/D. Aydemir

Kasar Japan da kungiyar Tarayyar Turai sun kulla sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da za ta shafi kashi daya bisa uku na tattalin arzikin duniya.

Masharhanta na ganin wannan a matsayin martani ga manufofin Shugaba Donald Trump na Amirka wanda ya dauki matakan kare harkokin kasuwanci na Amirka. Karkashin sabuwar yarjejeniyar za a zabtare galibin kudaden fito tsakanin kasashen Turai da Japan da kimanin kashi 99 cikin 100 daga kayayyakin da suke fitowa daga Japan zuwa Turai, sannan kimanin kashi 94 cikin 100 daga kayayyakin kasashen Turai da ake kai wa zuwa kasar Japan.