1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar jigilar fetur tsakanin Sudan biyu

August 4, 2012

Sudan ta amince Sudan ta kudu ta ci gaba da amfani da kasarta domin fitar da man fetur zuwa ketare, wanda aka dakatar a watan janairun 2012 sakamakon tsamin dangantaka.

https://p.dw.com/p/15jqA
--- DW-Grafik: Per Sander 2011_06_22_sudan_südsudan_öl_konflikt.psd
Hoto: Fotolia-Dark Vectorangel/DW

Tsohon shugaban Afirka ta Kudu Thabo Mbeki da ke shiga tsakani a rikicin Sudan da kuma Sudan ta kudu, ya bayyana cewar kasashen biyu sun amince su kawo karshen rikicin man fetur da ke tsakaninsu. A lokacin da ya ke yi bayani a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, Mbeki ya ce fadar mulki ta Khartum da kuma takwararta ta Juba za su ci gaba da tattaunawa tsakaninsu, da nufin tsayar da ranar da sudan ta Kudu za ta fara ratsa kasar Sudan domin jigilar man fetur ta i zuwa kasashen ketare domin sayarwa.

Tun dai watan janairu ne dai jaririyar kasar wato Sudan ta kudu ta dakatar da fitar da man da Allah ya hore mata, bayan rashin jituwa da ya taso tsakaninta ta Sudan game da yawan kudin da ya kamata ta biya domin amfani da bututan man hukumomin Khartum. Sai dai mai shiga tsakanin bai bayyana ko makobtan biyu wato Sudan da kuma Sudan ta kudu sun amince su kawo karshen rikicin kan iyaka da ke tsakaninsu koko a'a ba.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman