1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwadagon yara na ci gaba da zama kalubale a duniya

January 26, 2021

A ranar Alhamis (21.01.2021) kungiyar kwadago ta duniya ILO ta fara wani shiri ta kafar Intanet na "Shekarar Majalisar Dinkin Duniya don kawar da kwadagon kananan yara, maimakon zuwa makaranta.

https://p.dw.com/p/3oRLn
Symbolbild Kinderarbeit
Hoto: Imago Images/Pacific Press Agency/R. Sajid Hussain

Wannan shiri na da burin kara kaimi ga matakan da gamaiyar kasa da kasa ke dauka don kawo karshen kwadagon kananan yara kafin shekara ta 2025.

A wani karamin wuri da ke kusa da New Delhi babban birnin kasar Indiya, wata yarinya ce 'yar shekara 11 tare da 'yan uwanta na zaune  gaban gida tana dinke kwallo kafa. A rana tana iya dinke kwallaye guda biyu, tana samun centi 23 kwatankwacin Naira 120. Iyayenta sun dogara da kudaden da yaran ke samu.

Bisa kiyasin kungiyar kwadago ta duniya ILO, a fadin duniya yara kimanin miliyan 152 ne ke aiki dabam-dabam da suka kam a daga dinki, talla ko a gonaki ko kuma a aikin gine-gine, a cewar Thomas Wissing shugaban sashen kula da hakin dan Adam a bangaren kwadago a duniya.

Symbolbild Kinderarbeit
Yaro yana aiki a BangladashHoto: picture-alliance/NurPhoto/S. Mahamudur Rahman

Ya ce: "Kashi 90 cikin 100 na irin wadanan yara ana samunsu a kasashen Afirka da na Larabawa da kuma na Asiya. Kashi 10 cikin 10 sun kakkasu a Latin Amirka da Turai. Ya kamata yara su sami damar zuwa makaranta, saboda haka bai kamata su yi aiki har sai sun kai shekaru 15. Sai dai babu matsala idan aikin gida ne ko wasu ayyuka da ba su taka kara sun karya ba da za a iya yi cikin awa daya ko biyu a rana, wadanda kuma ba za su kawo cikas ga neman ilimin yaro ba."

Ga kungiyarta ILO dai annobar corona ta kara dagula halin da ake ciki a batun na kwadagon yara, sai dai ILO ta ce zai yi wuri a yanke hukunci na karshe. Ta ce akwai yara da suka rasa aikin yi sannan a daura da haka saboda dalilai na tattalin arziki wasu yaran na aiki don tallafa wa iyaye.

A cikin bururruka na muradu masu dorewa, kasashen duniya dai sun yi alkawarin yaki da kwadagon yara, su kuma kawar da shi kafin shekarar 2025. An fara samun nasarori, tun bayan shekara ta 2000 kwadagon yara ya ragu da kashi 38 ckin 100. Sai dai akai jan aiki a gaba kafin a kai ga kasar da shi baki daya inji Thomas Wissing na kungiyar ILO.

Kongo Kindersoldaten
Yara masu aikin soji a KongoHoto: picture-alliance/dpa/M. Gambarini

Ya ce: "A wasu kasashe akwai bukatar karfafa aikin masu bincike don gano inda ake saka yara aikin dole. A wasu kasashen  kudi ake bukata don fadada tsarin tallafa wa jama'a, a wasu kuma hadin kai ake bukata tsakanin kungiyar farar hula don kirkiro da wata hanya da za ta maye gurbin kwadagon yara. Akwai dai zabi da dama, amma muhimin abu shi ne samar da kyawawan ginshikan tattalin arziki ga iyalai domin su yi watsi da kwadagon yara."

Don cimma wannan burin dole nan da shekaru biyar masu zuwa a rage yawan yara da ake aiki da miliyan 30 a kowace shekara. A taron shekarar MDD ta kawar da kwadagon yara da aka fara ranar Alhamis ta kafar Intanet, za a gabatar da kwararan matakai da kowace kasa ta dauka bisa manufa.