1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yankunan gabashin Jamus, shekaru 16 bayan haɗewar ƙasashen Jamus ta Gabas da ta Yamma.

YAHAYA AHMEDOctober 3, 2006

A lokacin bukukuwan cika shekaru 16 da haɗewar Jamus, ministan sufuri da ayyuka da raya birane na tarayyar Jamus, Wolfgang Tiefensee, ya dubi irin ci gaban da aka samu a yunƙurin da ake yi na sake gina yankunan gabashin ƙasar da kuma irin matsalolin da ake huskanta.

https://p.dw.com/p/BvRM
Wolfgang Tiefensee, ministan sufuri da ayyuka da raya birane na tarayyar Jamus.
Wolfgang Tiefensee, ministan sufuri da ayyuka da raya birane na tarayyar Jamus.Hoto: AP

A ganin Wolfgang Tiefensee, ministan sufuri da ayyuka da raya birane na tarayyar Jamus, har ila yau da sauran rina a kaba, a yunƙurin da ake yi na sake gina yankunan gabashin Jamus don su kai matsayin yankunan yamma. Ba ministan kaɗai ne ke da wannan ra’ayin ba. Shahararrun masu binciken halin rayuwar jama’a a nan Jamus, kamarsu Gustav Horn ma na yi wa gabashin Jamus ɗin irin wannan kallon. Bisa cewarsa dai:-

„A yanzu, abin da muke gani a gabashin Jamus, bai bambanta da hasashen da muka yi daga farko zuwa tsakiyar shekarun 1990 ba, wato na cewa, za a sami wasu yankuna ɗaiɗai da za su farfaɗo. Amma gaba ɗaya, ba za a cim ma bunƙasar gabashin Jamus ɗin cikin gajeren lokaci ba. Har ila yau dai ana ta fama da haɓakar yawan marasa aikin yi, kuma jama’a da dama na yankin na ƙaura zuwa yamma.“

Da can dai waɗannan yankuna ɗai-ɗai da suka farafaɗo ne Wolfgang Tiefensee ke matashiya da su, inda kuma yake ganin za a iya bin misalansu wajen farfaɗo da sauran yankunan na gabashin Jamus, don su cim ma matsayin da yankunan yamma suka kai. Sai dai, gwamnatin tarayya ta janye daga goyon bayan wannan salon. Dalilin haka kuwa, shi ne gunagunan da tsoffin jihohin tarayya na yammacin Jamus ke yi game da maƙudan kuɗaɗen da ake ta turawa zuwa gabashin ƙasar, amma ba tare da cim ma buri ba. Kuɗaɗe ne kuma da su jihohin yamman ke ganin suna bukata don aiwatad da ayyukan raya nasu yankunan. Ministan ya amince da zargin da ake yi wa gwamnatocin jihohin gabashin Jamus ɗin, na rashin yin mafani da kuɗaɗen bisa ƙa’ida. Amma duk da haka, ya kuma ce a halin yanzu dai, ana samun ci gaba a wannan huskar:-

„A cikin ’yan shekarun da suka wuce, an aiwatad da ayyuka masu amfanin gaske. Idan aka dubi ayyukan da muka gudanar a cikin shekaru 16 zuwa 17 bayan haɗewar Jamus, za ka ga cewa a ƙarƙashin ƙasa, da kuma a sarari, mun samad da tituna, da kafofin kula da tsoffin mutane da naƙasassu, da asibitoci, da makarantu da jami’o’i. A huskar kare muhalli kuma, mun tsabtata koguna, waɗanda da can cike da gubar masana’antu suke, iskar da ake shaƙa a yanzu ma daban take, ga shi kuma mun inganta yanayin al’adu a duk faɗin yankin na gabashin Jamus. Kowa kuma na iya shiga cikin shagulgulan dimukraɗiyya.“

Duk da hakan dai, masharhanta da dama na ganin cewa, gabashin Jamus, yawan marasa aikin yi ya riɓanya na yammacin ƙasar har sau biyu. Kuma har ila yau, wurare da dama a gabashin Jamus ɗin ba su da ababan jin daɗin rayuwa kamar a yamma. Ko yaushe za a cim ma wannan burin na samun daidaito tsakanin yankunan biyu? A ganin minista Wolfgang Tiefensee dai:-

„Za a daɗe ana dauriya, kafin mu kai ga matsayin da jihohin gabashin Jamus za su iya tsayawa kan ƙafafunsu a huskar tattalin arziki. Muna dai bukatar kai ga wannan matsayin, saboda a waɗannan jihohin ma, akwai masu sha’awar ganin cewa, ba kawai tallafi za su dinga karɓa daga jihohin yamma ba. Su ma sun cancanci a ce suna ba da tallafi ga asusun raya wasu jihohin daban.“