1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yankin kudancin Sudan ya zama sabuwar ƙasa

July 9, 2011

Cikin wani ƙasaitaccen biki da ya sami halartar shugabanni daga sassan duniya a yau yankin kudancin Sudan ya ayyana yancin cin gashin kai a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.

https://p.dw.com/p/11sEY
Jamhuriyar kudancin Sudan ya zama ƙasa ta 193 a duniya

Yankin kudancin Sudan ya zama sabuwar ƙasa mai cin gashin kai. Bikin samun yancin yankin wanda ya gudana a yau ya sami halartar shugabanin ƙasashen Afirka 30 da man'yan jami'an gwamnatoci daga ƙasashen yamma, ciki har da sakatare janar na MDD Ban Ki-moon. shugaban ƙasar Sudan Hassan Omar Al-Bashir, wanda shima ya halarci kaddamar da sabuwar ƙasar, ya sami tarba da ga Silava Kiir Mayardit wanda ya kasance sabon shugaban jamhuriyar Sudan ta kudu.

Südsudan Unabhängigkeitserklärung
Faretin sojin kudancin Sudan a JubaHoto: ap

Bayan faretin sojojin kudanci an sauke tutar ƙasar Sudan aka ɗora Tutar sabuwar jamhuriyar Kudancin Sudan. Daga bisani tsohon madugun 'yan tawaye Salva Kiir ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban ƙasar Kudancin Sudan.

Südsudan Unabhängigkeitserklärung
Shagulgulan murnan 'yancin kai a kudancin SudanHoto: dapd

Kakakin majalisar dokin Sudan James Wani Igga shine ya yi jawabin ayyana sabuwar Jamuhuriyyar Sudan Ta kudu in da yace " Mu zaɓaɓɓu ta han'yar demokraɗiyya wakilan jama'a, bisa ga buƙatar mutanen kudancin Sudan, ta sakamakon ƙuri'ar jin ra'ayi muna ayyana Kudancin Sudan a matsayin mai yanci da cin gashin kai"

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita Abdullahi Tanko Bala