1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila za ta dauki fansa kan Iran

Suleiman Babayo USU
October 2, 2024

Gwamnatin Isra'ila ta ce tana shiye ta dauki matakin da ya dace na ramuwar gayya kan makaman roka da Iran ta harba mata, yayin da lamura ke kara rincabewa a yankin Gabas ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/4lJus
Kwafi mahada
Isra'ila | Bayan hare-haren Iran
Bayan hare-haren IranHoto: Amir Cohen/REUTERS

Gwamnatin Isra'ila ta yi barazanar cewa za ta dauki fansa game da makaman roka da Iran ta harba zuwa kasar. Wannan na zuwa lokacin da Iran ke cewa muddun Isra'ila ta yi yunkurin kai mata hari, za ta lalata kayayyakin more rayuwa na Isra'ila. Ana sa bangaren Shugaba Joe Biden na Amurka ya ce kasarsa tana ba da cikekken goyon baya ga Isra'ila bayan hare-haren na Iran. Ita dai Iran ta cilla kimanin rokoki 200 a kan Isra'ila inda galibi dakarun Isra'ila da kawanta suka kakkabo.

Kafofin yada labaran kasar ta Iran sun ruwaito cewa ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya tattauna da takwarorinsa na kasashen Turai jim kadan bayan kasarsa ta kaddamar da farmakin rokokin kan Isra'ila, kuma ya tabbatar da cewa kasarsa ta kammala hare-haren kan Isra'ila.

A wannan Laraba dakarun na Isra'ila sun kaddamar da sabbin hare-hare kan birnin Beirut fadar gwamnatin Lebanon, kan abin da suka kira wuraren 'yan ta'adda. Tuni yanayin da ake ciki ya haifar da tsoron yuwuwar barkewar yaki a yankin Gabas ta Tsakiya wanda zai iya fadada fiye da yadda ake tunani.