1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yanayin sanyin bana a nahiyar Turai ya karu

February 5, 2019

Nahiyar Turai na ganin sauyi a yanayin sanyi na bana idan aka danganta da yadda yake a shekarun da suka gabata.

https://p.dw.com/p/3CkDu
Wintereinbruch Schnee Türkei
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Celik

Yanayin sanyi a nahiyar Turai a bana, ya yi kamarin da aka jima ba a ga irinsa ba, duba da yawan dusar kankarar da ake samu da kuma irin yadda ta haddasa tsaiko ga wasu harkoki da aka saba na yau da kullum.

Sai dai duk da wannan kamari da sanyi ya yi, wasu Jamusawa na amfani da lokacin don fita wuraren da ke da tsaunuka suna wasannin zamiyar kankara tare da 'ya'yansu a wani tsari na nishadi ta hanyar amfani da wannan yanayi.