1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan'adawa a kasar Laberiya sun yi watsi da sakamakon zabe

October 15, 2011

Wasu jam'iyyun siyasa guda tara sun ce an tabka magudi wajan baiyana sakamakon zaben

https://p.dw.com/p/12sm5
Winston Tubman jagoran 'yan adawa a LaberiyaHoto: picture alliance/dpa

Yan adawa a kasar Laberiya sun yin watsi da sakamakon zabe wanda hukumar da alhakin gudanar da zaben ya rataya akan wuyanta wato NEC ta ke baiyanawa.A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da janm'iyyun siyasar guda tara suka baiyana a ciki harda jamiyyar Winston Tubman; jagoran jamiyyar masu neman canji ta CDC mutumin da da farko ake jin cewa zai fafata da Ellen Johnson Sirleaf a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar.

Sun ce an shirga makudi wajan baiyana sakamakon tare da yin kira ga wakilansu dake cikin hukumar da su kauracemata. An dai shirya jamiyyun guda tara zasu gudanar da wani taro a gobe lahadi domin fatikar da magoya bayansu dakuma jakadun kasashen duniya a laberiya akan matakin da suka dauka. A ci gaban baiyana sakamakon zaben na yan majalisun dokoki da na shugaban kasar da aka gudanar a ranar 11 ga watan Oktoba .Fitaciyar shugabar kasar Elene itace ke gaba

da kashi 45 cikin dari na kuriun da aka kada yayin da jagoran yan adawar tubman ke da kashi 29 sannan sai prince wanda ya zo na ukku da kashi 11 wanda kuma ya ke tare da gungun jamiyyun siyasar na adawar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita Zainab Mohammed Abubakar