1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan zanga zangar Siriya sun bukaci janye shugaban tawagar kungiyar kasashen Larabawa

December 30, 2011

Masu adawa da gwamnatin Siriya sun zargi tawagar 'yan sa ido na kungiyar kasashen Larabawa da nuna son rai

https://p.dw.com/p/13c1x
Mustafa al-Dabi shugaban tawagar kungiyar kasashen Larabawa a Siriya
Mustafa al-Dabi shugaban tawagar kungiyar kasashen Larabawa a SiriyaHoto: picture-alliance/dpa

A kasar Siriya masu zanga-zangar nuna adawa da gwamnati sun yi kira da a gudanar da zanga-zanga a fadin kasar domin nuna rashin aimncewa da tawagar 'yan sa ido da kungiyar kasashen Larabawa ta tura zuwa kasar. 'Yan adawa na sukan tawagar ne da rashin daukar matakin kau da ci gaban tashin hankalin da aka fuskanta a daidai lokacin da take ziyara a wannan kasa. Kakakin 'yan adawar ya yi kira d a janye shugaban tawagar yana mai bayyana tsoron cewa General Mustafa Al Dabi da ke wa tawagar jagora na nuna son rai a aikinsa. Bayan da tawagar ta isa birnin Homs inda rikicin ya fi kazanta an rawaito Al Dabi na fadar cewa babu wani abin damuwa da ya gano a wannan wuri.

Shi dai shugaban tawagar amini yake ga shugaba Omar Albashir na Sudan da aka ba da sammace akansa bisa laifin aikata kisan kiyashi. Wadanda suka shedar wa idanusa sun ce ana ci gaba da dauki-ba-dadi tsakanin 'yan zanga -zanga da dakarun tsaron Siriya.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Dan-Ladi Aliyu